Kutsen Vtech: yan sanda sun damke wani mutum

Image caption Kamafanin Vtech ya shawara wajen samar da kayan wasan yara tun daga motoci zuwa kananan komfutoci

'Yan sanda masu binciken kutsen da aka yi wa kamfanin Vtech mai kera kayan wasan yara sun kame wani mutum dan shekara 21 a Berkshire a Britaniya.

Ana tsare da mutumin ne bisa zargin yin amfani da wata komfuta ba tare da izini ba, a cewar hukumar kula da manyan laifuka na kudu maso gabashi watau SEROCU.

A tsakiyar watan Nuwamba ne a ka yi kutse cikin rumbun ajiye bayanan masu huldar kasuwanci da kamfanin na Vtech.

A jimilla, bayanan abokan kasuwancin kamfanin miliyan 6 ne aka sata.

A cewar Craig Jones shugaban kula da tsaro na SEROCU "har yanzu muna binciken farko kan matsalar kuma da akwai sauran aiki".

"Laifukan da suka shafi intanet, manyan matsaloli ne ba su da iyaka na kasa da kasa, sun shafi mutane da yawa a mataki na gida da kasa da kuma duniya baki daya" a cewarsa.

Kutsen da aka kai wa kamfanin ya shafi rumbun ajiye bayanai wanda ke tallafar manhajarsa ta koyarawa.

Manhajar na ba abokan cinikin kamfanin wadanda su ka yi rajista da shi damar su sauko da karin bayanai da wasanni da littafan da ake karanta su a komfuta ga na'urarsu ta hannu.

Kamfanin Vtech na sayar da kayayyakin wasan yara da suka hada da motoci da masu amfani da lantarki kamar kyamarori da kananan komfutoci da wasanni da kuma littafan da ake karantawa a komfuta.