Ana gwajin na'ura mai gane fuskar barawo a Biritaniya

Image caption Sabuwar fasahar na iya gane fuskar mutane cikin sauki idan babu gilashi a idnunsu

BBC ta samu labarin cewa wani tsari da kantunan Biritaniya ke amfani da shi wajen gane bata gari ko barawo a kantunansu na shirin gwajin wata fasahar gane fuskar masu laifi da zaran sun shiga kantunan.

Kafin yanzu, fasahar gane fuskar mutane mai suna facewatch ta ba 'yan kasuwar na cikin gida a Biritaniya wata sabuwar hanyar rarraba hotunan bidiyo da kyamarorin daukar hoton shige da ficen mutane a kantunansu, suka dauka na masu yi musu sata da kuma masu aniyar yin hakan daga kamaninsu.

Yanzu fasahar na iya aikawa masu kantunan wasu sakwanni da zarar fasahar gane fuskar ta gano fuskar wani bata gari da ta yi daidai da na wadanda aka rarrabawa masu kantunan da ke cikin tsarin a yankin.

Fasahar facewatch na taimakawa 'yan kasuwa a yankinsu kirkira da kuma rarraba hotunan barayi da masu yi dauke-dauke a kantunansu, ko kuma sanannun barayin jaka.

Tsarin wanda sama da wuraren kasuwanci 10,000 su ka yi rajista da shi, ya na taimakawa 'yan kasuwa aikawa da hotunan da kyamarar ta dauka ga 'yan sanda.

A da, gane fuskar maras gaskiya ya dogara ne ga sa idon ma'aikata, amma fasahar facewatch na duba fuskokin duk wanda ya shigo kanti da kuma sa alamar dan akwati a fuskar da ta gane na bata gari ko barawon jaka.