Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

'Yan Shi'a sun yi watsi da kwamitin 'yan sanda

Kungiyar 'yan Shi'a a Najeriya ta yi watsi da kwamitin da aka ce babban sufeton 'yan sandan kasar ya kafa domin ya binciki tashin hankalin da aka yi a Zariya.

Haka kuma kungiyar ta yi kira ga hukumomin kasar, su mika mata shugabansu Malam Ibrahim El-Zakzaky da yanzu haka yake hannun sojoji.

Malam Yakubu Yahaya Katsina, daya daga manyan shugabannin 'yan Shi'a a kasar, shi ne ya bayyana wa BBC matsayinsu kan wannan bincike da gwamnati ke shirin yi.