shia
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Shi'a: Kada dai kilu ta jawo Bau

A Najeriya, yayin da ake ci gaba da maida martani a bisa rikicin nan da ya wakana a kasar tsakanin sojoji da 'yan Shi'ah, kungiyar mabiya addinin kirista ta kasa CAN ta yi kira ga hukumomi a Najeriya da su bincika musabbain kashe-kashen da aka yi, don hana rikidewar rikicin zauwa wani abu dabam. Kungiyar ta nemi a koyi darasi daga rikicin Boko Haram. Kungiyar Muslmi ta jamaatul Nasrul Islam ma dai ta fitar da wata sanarwa inda ta yi kira makamancin wannan. Daga Kaduna ga rahoton wakilinmu Nurah Mohammed Ringim.