Amfani da fasahar kwamfuta a tasoshin bas a London

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Fasinjoji za su iya ganin hanyoyin da motar bas za su bi da kuma lokuta kai tsaye daga tashar bas din

An kafa allunan sanarwa na komfuta masu aiki da hasken rana a tasoshin motocin safa a matsayin gwaji.

Allunan da aka kafa, suna dauke da bayanai na motocin bas-bas din da ke bin hanyar kai tsaye ga fasinjojin da ke jira a tashar.

Bayanan sun kunshi lokacin da motar bas din za ta iso tashar, da adadin mintuna da fasinjojin za su jira wata bas din.

Fasinjojin za kuma su iya ganin hanyoyin da bas din za ta bi da kuma lokuta.

An kafa sabbin na'urorin na allunan a tasoshi hudu a matsayin gwaji, nasarar hakan za ta sa a kafa su a sauran tasoshi kimanin 9,000 a Biritaniya