An yi kutse a tsarin karbar kudi na otal din Hyatt

Image caption Otal din Hyatt ba shi ne na farko da ya gamu da mtsalara tsaro a intanet ba

Rukunin kamfanin otel din Hyatt ya gargadi masu mu'amala da shi cewa an yi kutse cikin tsarin biyan kudinsa.

Kamfanin ya ce ya gano wata manhajar satar bayanai a cikin tsarin karbar kudade daga masu mu'amala da shi a otal-otal din da ke karkashinsa.

Shugaban kula da ayyuka na rukunin kamfanin Hyatt na kasa da kasa Mista Chuck Floyd ya ce an magance matsalar, amma ya shawarci wadanda su ka yi hulda da shi da su binciki asusun ajiyar bankunan ko an taba.

"Da zaran mun gano abin da ya faru sai muka kaddamar da bincike" a cewar shugaban.

Rukunin kamfanin na Hyatt mai shalkawata a Chicago a Amurka na da otal-otal 627 a karkashi kulawarsa, ko da yake ya ce 318 ne wadanda ya ke kula da su kai tsaye wannan kutse ya shafa.

Amma kamfanin bai ce ko kutsen ya sa an kai ga wasu bayanan da suka shafi wani mai mu'amala da shi ba, sai dai sun dauki wani masani a kan tsaro a intanet mai zaman kansa wanda zai gudanar da bincike.

Kamfanin Hyatt ya bude wani shafin intanet domin ci gaba da sanar da masu hulda da shi kan halain da ake ciki game da lamarin.

Hyatt ba shi ne otal na farko da ya gamu da wannan matsala ta tsaro ba intanet.

Otal din Hilton da Mandarin da Starwood da kuma rukumin kamfanonin otal-otal na Trump duk sun ci karo da irin wannan matsala ta tsaro da ta shafi karbar kudi daga masu hulda da su a shekara ta 2015.