Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Karancin man fetur ya ta'azzara a Nigeria

A Najeriya a yayin da karancin Man fetur ke ci gaba da addabar jama'ar kasar, dillalan Man fetur masu zaman Kansu tare da hukumar da ke kula da sayar da mai a kasar DPR na ci gaba zargin juna a bisa batun na karancin mai a kasar.

A yayin da hukumar dake kula da sayar da man Fetur DPR ke zargin dillalan mai da boye shi da kuma tsawwala farashi har ma ta kai sukan bayar da man da aka boye kyauta ga jama'a, dillalan mai na cewa rashin aikin matatu da sauran matsaloli na gudanarwa ne ummulhabaisin karancin mai.

Ga rahoton Yusuf Ibrahim Yakasai