An yi wa shafukan BBC Kutse

Image caption Sakon da masu ziyartar shafukan BBC su ka taras a intanet yayin da aka yi kutsen

Dukkanin shafukan BBC na intanet sun kasance ba sa aiki a safiyar Alhamis sakamakon wani gagarumin kutse.

Matsalar ta faru ne da misalin karfe 7:00 na safiyar ranar Alhamis a inda masu ziyartar shafukan intanet na BBC su ka ci karo da wani sako da ke nuna kuskure a maimakon shafukan da suka saba gani.

Wasu majiyoyi a cikin BBC sun ce bacewar shafukan a intanet sakamakon wani salon kutse ne da ake yi wa lakabi da "hana aiki na bai daya"

Wata sanarwa da BBC ta fitar a dandalin aika sakwanni na Twitter ta dora laifin batan shafukan ne a kan wata "matsala da ta shafi aiki".

A cikin sakon, BBC ta ce ta na sane da faruwar matsalar, kuma tana iya bakin kokarinta na shawo kan lamarin da kuma ganin cewa shafukan sun ci gaba da aiki, ana kuma ganinsu kamar yadda aka saba.

Da tsakar rana, sai hukumar gidan rediyon ta sake fitar da wata sanarwa mai cewa "yanzu shafukan BBC suna aiki kamar yadda suka saba".

"Muna neman afuwa dangane da matsalolin daukewar shafukan suka haifar muku da kuma rashin jin dadi ". In ji sanarwar.

Hukumar BBC ta ki ta amsa ko musa zargin cewa kutsen da aka yi shi ya haifar da matsalolin.

Kutsen da aka yi wa babban shafin na BBC da kuma wasu ayyuka da ke tare da su, manhajar saurare ta iPlayer da kuma iPlayer ta radio sun daina aiki yadda ya kamata.

Martanin masu amfani da dandalin sada zumunta da muhawara na intanet ya zo cikin gaggawa, yawancinsu sun yi kira ga BBC da su dau mataki na gaggawa na gyara shafukan, sannan sun koka dangane da yadda gyaran ke daukar tsawon lokaci.

Da misalin karfe 10:30 na rana shafukan sun dawo, sun kuma soma aiki duk da cewa wasu sun dauki tsawon lokaci kafin su bude.

A baya, shafukan BBC sun taba samun irin wannan matsalar, a watan Yuli na 2014, manhajar iPlayer da sauran wasu shafukan an daina ganinsu a intanet tsawon kwanakin karshen mako na Asabar da Lahadi.