Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Tankiya tsakanin Saudiyya da Iran

Al'ammuran Diplomasiyya sun dagule matuka a Gabas Ta Tsakiya, bayan Saudiyya ta katse huldarta da Iran, sakamakon kisan wani fitaccen malamin Shia a Saudiyyar.

Bahrain da Sudan su ma sun yanke huldarsu da Iran din, kuma Hadaddiyar Daular Larabawa ta rage yawan ma'aikatanta da ke kasar ta Iran.

Ma'aikatar harkokin wajen Iran din ta zargi Saudiyya da tada fitina a yankin. Ga rahoton Aichatou Moussa.