Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

'Mun yi aure a sansanin Dalori a Maiduguri'

Duk da irin yanayin da ake ciki a sansanin Dalori, wasu sun shiga fagen soyayya. Modu Bulama mai shekaru 35 ya je sansanin ne bayan da’yan Boko Haram suka kashe matarsa da ‘ya’yansu biyu. A lokacin da yake aikin bada taimako wajen rarraba kayan agaji a sansanin, sai ya hadu da matarsa, wacce ita ma aka kashe mata miji a rikicin. Bayan sun ji labaran juna, sai suka amince su yi aure. Ya biya sadakin dala hamsin kafin su yi auren.