Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Gane mini hanya 09/01/2016

Ma'aikatar lafiya ta Najeriya ta ce annobar cutar zazzabin lassa ta kashe mutane 40 a jihohi 10 na kasar.

Ma'aikatar lafiya ta Najeriya ta ce annobar cutar zazzabin lassa ta kashe mutane 40 a jihohi 10 na kasar.

Hukumomin lafiyar sun ce kimanin mutane 150 ne suka kamu da cutar a jihohin Kano da Bauchi da Taraba, da Neja, da Ribas da Oyo da kuma Edo.

Masana kiwon lafiya na cewa cutar mai saurin yaduwa tana da matukar hadari, kuma tana kamanceceniya da cutar Ebola.

Akan haka ne wakilin mu a Kano Yusuf Ibrahim Yakasai ya tattaunawa da Dr. Nasiru Sani Gwarzo babban jami'i a ma'aikatar lafiya ta Nigeria kan yanayin cutar, da matakan da ya kamata a dauka domin kauce mata, sannan da abubuwan da ya kamata jama'a su yi idan wani na su ya kamu da cutar.