Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

'Yan sanda a Kano sun yi babban kamu

Rundunar 'yan sanda a jihar Kano ta ce ta kwato miyagun kwayoyi da suka kai Naira biliyan daya da miliyan dari 200 a cikin watanni biyu da suka wuce.

Rundunar ta ce ta kuma yi nasarar damke dillalan kwayoyi ciki har da masu dilar hodar ibilis.

Wakilinmu Yusuf Ibrahim Yakasai, ya tambayi kakakin rundunar Magaji Musa Majiya karin bayani kan wannan kame da suka yi.