Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Majalisar koli ta gana da El-Zakzaky

Majalisar koli ta addinin Musulunci a Najeriya ta bayyana cewar ta gana da Sheikh Ibrahim El-zakzaky da uwargidansa a inda suke tsare.

Daya daga cikin mambobin majalisar Farfesa Dahiru Yahaya wanda ke cikin tawagar da ta gana da ElZakzaky, ya shaida wa BBC cewar, shugaban na 'yan Shi'a ya soma murmurewa daga harbin bindiga da aka yi masa.