Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Obama ya kare matsayinsa a Amurka

Shugaba Obama ya yi matukar kare irin abubuwan da yayi a kan mulki, a jawabinsa na karshe ga majalisun dokokin Amurka. Ya ce yana da kyakyawan fata game da makomar kasar. Amma kuma ya jaddada cewa, manufofin Amurkar game da kasashen waje, ba zasu tsaya kawai ga dakile barazanar da ake fuskanta daga kungiyar IS da Al Qaeda ba. A cewar shugaba Obama, za a ci gaba da tashin hankali a sassa da dama na duniya, na tsawon shekaru dayawa. Ga rahoton Jimeh Saleh.