Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Gane Mini Hanya 23/01/2016

A Nijeriya, tun bayan da wasu daga cikin 'yan matan da 'Yan Boko Haram suka sace a Chibok suka kubuta, gwamnatoci da kuma kungiyoyi masu zaman kansu, suke ta daukar matakai na taimaka wa wadannan 'yan mata su sama da hamsin. Paul Gadzama da maidakinsa Rebecca ma na daga cikin masu taimakawa irin wadannan 'yan mata, domin kuwa a halin da ake ciki sun kasance sanadiyar samun guraben karo karatu a Amurka ga wasu daga cikin 'yan matan Chibok din . Lokacin wata ziyara da suka kawo nan sashen Hausa na BBC, Ahmad Abba Abdullahi ya tattauna da su, inda ya fara da jin dalilinsu na neman agaza masu.