Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Muhimman bayanai kan cutar Zika

Hukumar lafiya ta Duniya ta ce tana sa ran kwayar cutar nan ta Zika, wadda wani nau'in sauro ke bazawa, za ta yadu zuwa dukan kasashen nahiyar Amurka, in ban da Canada da Chile.

Annobar cutar dai, wadda aka alakanta da haifuwar gilu, watau jariri mai karamin kai, tana yaduwa cikin sauri a Brazil- kasar da za ta dauki bakuncin wasannin Olympics a karshen shekara.

Kwararru sun ce kwayar cutar na yin illa ga bunkasar kwakwalwar dan tayi.

Ga dai Jimeh Saleh da karin bayani a kan yanayin wayar cutar.