Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

An kai harin kunar bakin wake a Chibok

Rahotanni daga Chibok a jihar Borno na cewa an samu hasarar rayuka da kuma jikkatar jama'a a sakamakon fashewar wasu bama-bamai.

A garin na Chibok ne a 2014 aka sace 'yan mata dalibai su sama da dari biyu, wadanda har yanzu ba aji duriyar galibinsu ba.

Ahmad Abba Abdullahi ya tuntubi Malam Ayuba wani dan garin na Chibok, wanda ya ce duk da ba ya cikin garin a yanzu, amma yana da bayani kan abin da ya faru: