Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

'Yadda kamfani na ya bunkasa a Lagos'

Shirinmu na Matan Afrika zai ci gaba. Kamar yadda muka shaida muku a baya, a wannan kashi na biyu na shirin matan Afrika masu matsakaitan sana'o'i, zamu gabatar muku da mata takwas ne wadanda suke kokarin sun samu abin rufin asirin rayuwa.

Wannan ce fitowa ta hudu ta wannan kashi, kuma za mu ji daga bakin wata mata Affiong Williams da ke birnin Lagos a Najeriya. Ita ce shugabar kamfanin ReelFruit, wanda yake samar da kayan kwalam da makulashe da kuma sarrafa kayan marmari masu dadi ga mutanen da ke neman irin abincin da zai taimaka wajen inganta lafiyarsu