Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

An soma shari'ar Gbagbo a kotun ICC

A karon farko tsohon shugaban wata kasa ya gurfana a gaban kotun duniya mai shari'ar mugayen laifufuka.

Ana tuhumar Laurent Gbagbo, tsohon shugaban Ivory Coast, da aikata mugayen laifufuka hudu a kan jama'a.

Ya ki ya amince da sakamakon zaben shugaban kasar na watan Nuwamban dubu biyu da goma.

Hakan ya janyo rikicin da yayi sanadiyyar mutuwar mutane kimanin dubu uku a Ivory Coast din. Ga rahoton Jimeh Saleh: