Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Biritaniya ta amince a jirkita kwayoyin halittar dan-tayi

A karon farko a tarihi, masana ilimin kimiyya a nan Birtaniya sun sami izinin jirkita kwayoyin halittar dan tayi.

Za su yi bincike a kan dan tayin, don gano irin dalilan da su ke sa mai ciki ta yi raggon kaya, da kuma abin da ke faruwa a kwanakin farko da daukar cikin.

To amma in ji masu sukar wannan fasaha, somin tabi ne na halatta zayyana yadda ake son jarirai su kasance.

Ga rahoton Suwaiba Ahmed: