Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Yajin aikin masu biredi a Kano

A Najeriya, farashin biredi ya tashi a jahar Kano, sakamakon yajin aikin gargadi da kungiyar masu gidajen burodi ta jihar ta yi, saboda tsadar kayayakin hada burodin.

Yau suka kammala yajin aikin na kwanaki uku. To sai dai in ji Hausawa, ba a bari a kwashe daidai: matakin ya haddasa karancin biredin, da kuma hauhawar farashinsa.

Ga wannan rahoton na Yusuf Ibrahim Yakasai, wanda ya aiko mana a lokacin ana yajin aikin: