Ana yawan satar shanu a Kaduna
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

'Ana kawar da bata-gari a Kaduna'

Gwamnatin jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya ta kara jaddada aniyar ta, ta ci gaba da yaki da barayin shanu da masu aikata miyagun laifuffuka.

Matsalolin da ke addabar jihar sun hada da barayin shanu a dazukan da ke karamar hukumar Birnin Gwari da kewaye.

Shugaban 'Operation Yaki', Kanar Yakubu Yusuf, ya shaidawa BBC cewa "Jihar Kaduna na da matsaloli da yawa amma yanzu ana shawo kan matsalar inda aka murkushe bata-gari a unguwanni da dama."

Bayan kammala kashi biyu na yaki da barayin shanu a dajin Kamuku, wasu daga cikin barayin sun koma satar jama'a da fashi da makami a wasu sassa na jihar Kaduna, musamman a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Ikirarin na jihar Kaduna dai na zuwa ne a yayin da wasu ke cewa yaki da barayin shanun na cin karo da wasu matsaloli.

Daga Kaduna ga rahoton wakilinmu Nurah Mohammed Ringim.