Ken Nnamani
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ken Nnamani ya raba gari da PDP

Tsohon shugaban majalisar dattawan Najeriya, Ken Nnamani, ya yi shelar ficewa daga babbar jam'iyyar adawar kasar, wato PDP.

Mista Nnamani, wanda ya shugabanci majalisar dattawan daga shekarar 2005 zuwa 2007, ya ce ya bar jam'iyyar ne saboda ta rasa alkibla da shugabanci nagari.

A cewarsa, ya yi iyakar kokarinsa domin a samu canji a jam'iyyar don samo mata akida, amma bai yi nasara ba.

Ga karin bayani daga bakin Aliyu Abdullahi Tanko