Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

'Abin da ya sa Nigeria ta kori sojoji 250'

Wasu sojoji a Najeriya na kokawa saboda korar su da suka ce hukumomin sojin kasar sun yi a karo na biyu bayan 'yan watanni da dawo da su bakin aiki.

Sojojin su 250, na cewa ne bayan sake dawo da su sanadiyyar yafe musu laifuffukan da suka yi a arewa maso gabashin kasar yayin da suke yaki da Boko Haram.

Sojojin zargin cewa laifuffukan da ya sanya aka sake korar su bai taka kara ya karya ba.

A martaninsa, Kakakin sojin kasar, Kanar Sani Usman Kuka-sheka ya ce sojojin da aka kora sun gudu ne lokacin da aka bayyana musu cewa za su koma fagen yaki.

Ga karin bayani