Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

'Yan Najeriya na tuna Janar Murtala

A Najeriya a yau ne ake bukukuwan tunawa da tsohon shugaban kasar Marigayi Janar Murtala Ramat Muhammad.

A ranar 13 ga watan Augusta 1976, aka kashe marigayin, a wani yunkurin juyin mulkin da bai yi nasara ba.

Ana dai yin bikin tunawa da Murtala Muhammad ne sakamakon gudunmuwar da ya bayar wajen gina Nijeriya, musanman ta fukar yaki da cin hanci.

Janar Murtala Muhammad ya bar duniya yana da kimanin shekaru 37 da haihuwa, an kuma yi jana'izar sa tare da binne shi a mahaifarsa da ke Kano.

Ga rahoton wakilin mu Yusuf IUbrahim Yakasai daga Kano