Matsan Jamhuriyar Nijar
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Abin da ke damun matasan Nijar

A jamhuriyar Nijar, yayin da ake shirye-shiryen gudanar da zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar dokoki , matsalar rashin aikin yi musamman tsakanin matasa na ci gaba da daukar hankali saboda girman matsalar da kuma illar da take yi wa kasar.

Matsalar rashin aikin yi dai ta sanya 'yan Nijar din da dama kan tafi ci-rani a kasashe daban-daban musamman ma makwabta kamar Najeriya da Libya da Algeria da dai sauransu, inda sukan fada cikin mummunan yanayi, har ma da asarar rayukansu saboda wahala.

Wakilinmu Ishaq Khalid ya duba mana matsalar ta rashin aikin yi a jamhuriyar Nijar, ga kuma rahoton da ya aiko mana daga kauyen Tsaouni na jihar Damagaram.