Market Fire
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Gobe ta kone shaguna a kasuwar Singa a Kano

Wata gobarar da ta tashi a kasuwar kayayyakin masarufi ta Singa da ke Kano a arewacin Najeriya, ta kone kimanin shaguna dari biyu.

Gobarar dai ta fara ne tun misalin karfe biyar na asubahin ranar Alhamis, ta shafe fiye da sa'o'i bakwai tana ci.

Gobarar ta kone kayayyaki da kudade da aka kiyasta sun kai miliyoyin nairori.

Shugaba Muhammadu Buhari ya aike da sakon jajensa ga mutanen da gobarar ta shafa.

Wakilinmu na Kano Yusuf Ibrahim Yakasai na dauke da rahoton.