achaba in kaduna
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Kaduna: 'Yan Achaba sun dawo

A Kaduna yin goyo da kuma haya da babura watau Achaba sun dawo bayan kimanin shekara guda da hana wa.

An fi ganin wannan dabi'a ne a wasu manyan garuruwan jihar, kamar Kaduna da Zaria, da kuma Kafanchan.

Wakilin BBC ya lura da cewa matasa sun yi biris da dokar, domin har tashoshi na Achaban da aka haramta sun dawo.

Gwamnatin da ta gabata ce ta kafa dokar hana Achaban domin inganta tsaro a jihar.

Ga rahoton wakilinmu Nura Ringim