Babban sufeton 'yan sandan Najeriya
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

An kashe jami'in APC da iyalinsa a Ribas

'Yan bindiga sun kashe wani jami'in jam'iyyar APC a jihar Ribas, Mista Frankiline Obi, da matarsa da kuma dansa.

Mista Obi, wanda shugaban jam'iyyar APC ne na unguwa (Ward 4) a garin Omoku, an kashe shi ne lokacin da 'yan bindigar suka kai hari a gidansa.

Jihar Ribas dai na fama da ringimar siyasa tsakanin jam'iyyar PDP, mai mulkin jihar, da APC, mai adawa da ita a jihar amma ta na rike da gwamnatin tarayyar kasar.

Ga cewar 'yan sanda, 'yan bingidar sun harbe Mista Obin ne kafin su yanke kansa su tafi dashi.

Haka kuma sun harbe matarsa har lahira da kuma dansa, wanda shi ma yanzu ya mutu a asibiti a sabilin harbin.

Kakakin rundunar 'yan sanda a jihar ta Ribas, DSP Ahmed Kidaya Mohammed, ya gaya wa Abdullahi Tasiu Abubakar cewa cikin dare ne ran Asabar 'yan bindigar su ka shiga gidan Mista Obin.