zuma and buhari
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Za mu mayar wa Nigeria kudinta — Zuma

Shugaban Afrika ta Kudu Jacob Zuma ya tabbatar da cewa har yanzu kasarsa ba ta maida wa Najeriya kudi fiye da dala miliyan tara da jami'an tsaron kasarsa suka kama cikin wani jirgin Najeriya a shekara ta 2014 ba.

Bayan kama jirgin dai, shugaban Najeriya na wancan lokacin ya ce an tafi da kudin ne da saninsa zuwa Afrika ta kudu domin sayen makamai.

Da yake magana da manema labarai a yayin ziyarar kwanaki biyu da ya kammala a Najeriya yau din nan, Shugaba Zuma ya ce gwamnatinsa a shirye take ta mayar wa Najeriya da kudaden, idan hukumomin kasarsa suka kammala bincike.

Ga Haruna Shehu Tangaza dauke da karin bayani: