Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Rarrabuwa a tsakanin magoya bayan Hama Amadou

A jamhuriyar Nijar yayin da lauyoyin Hama Amadou ke cewa zai je zabe, jam'iyyar shi Moden FA Lumana cewa tayi hakan bata taso ba tukun, har sai an sako shi daga gidan yarin da yake.

A taron manema labarai da jam'iyyar ta kira, kakakinta Mahaman Laouali Leger ya fadawa wakiliyarmu Tchima Illa Issoufou cewa Hama Amadou ma na bayan matakin da COPA ta dauka na kauracewa Zaben.