Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Gane mini hanya 14/03/2016

A Jamhuriyar Nijar, hukumar zaben kasar CENI ta ce ta fuskanci matsaloli da dama a zaben shugaban kasa zagaye na farko da aka gudanar a ranar 21 ga watan Fabrairun da ya gabata.

Matsalolin dai sun hada da rashin bude wasu rumfunan zabe a kan lokaci da kuma karancin kayayyakin zabe, da rashin sanin makamar aikin daga wasu jami'an zaben tare da wasu matsaloli da dama.

A filin Gane Mani Hanya na wannan makon, wakilinmu BARO ARZIKA a Yamai ya tattauna da shugaban hukumar zaben CENI mai shari'a Bube Ibrahim wanda ya ce za su gyara wadannan matsalolin ta yadda za a yi zaben shugaban kasar zagaye na biyu ba tare da fuskantar wasu matsaloli ba;