Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Kokarin farfado da masa'antu a Nigeria

Tattalin arzikin Najeriya, wanda shi ne mafi girma a Afrika, yana jin jiki a sakamakon faduwar farashin mai a kasuwannin duniya. Yanzu haka cigaban tattalin arzikin na tafiyar hawainiya, fiye da a kowanne lokaci a cikin shekaru goman da suka wuce. Yanzu dai gwamnatin Najeriyar na son ta rage dogaro da man fetur ta hanyar farfado da masana'antun kasar da suka durkushe, kamar masaku. Ga dai rahoton Yusuf Yakasai daga Kano.