Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

'Yan kunar bakin wake sun halaka mutane a Masallaci

Hukumomin Najeriya sun ce wasu mata biyu 'yan kunar bakin wake, sun hallaka mutane akalla 24 a wani masallaci a kauyen Umarari da ke wajen Maiduguri babban birnin jihar Borno. Wasu karin mutanen 17 kuma sun samu raunika a hare-haren. Ya zuwa yanzu dai babu kungiyar da ta dauki alhakin kai hare-haren, amma ana kyautata zaton aikin 'yan Boko Haram ne. Ga dai Usman Minjibir da karin bayani daga Abuja.