Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Kalubalen shirya zabe a Nigeria - Jega

A ranar Lahadin nan mai zuwa ne za a gudanar da zabuka a wasu kasashen Afirka, kama daga zaben shugaban kasa a Congo-Brazaville, da zagaye na biyu na zaben shugaban kasa a Nijar da Benin da sake zaben shugaban kasa a Zanzibar na Tanzania, zuwa ga zaben raba-gardama a Senegal.

Yayin da ake shirye-shiryen wadannan zabuka ne kuma tsohon shugaban hukumar zaben Najeriya, Farfesa Attahiru Jega, ya gabatar da wata kasida a Londan, a kan yadda za a tabbatar da zabe mai nagarta a Afirka.

Abokiyar aikinmu ta BBC Focus on Afirka, Sophie Ikenye, ta tambayi Farfesa Jega kalubalen da ya fuskanta wajen shirya zabukan 2015 a Najeriya.