Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Gane Mani Hanya 19/03/2016

Gwamnan jihar Niger da ke arewacin Najeriya, Alhaji Abubakar Sani Bello, ya ce kawo yanzu gwamnatinsa ta kwato kusan naira miliyan 500 daga jami'an tsohuwar gwamnati wadanda ake zargin sun sace daga kudin fansho.

Gwamnan wanda ya kawo mana ziyara a ofishinmu na London, ya ce su na ci gaba da kokarin ganin sun kwato kudaden daga hannun mutanen da ake zargi domin aiwatar da ayyukan da ya sa a gaba a jihar.

A filin Gane Mane Hanya na wannan makon, gwamnan Abubakar Bello ya tattauna da Aliyu Abdullahi Tanko, a kan batutuwa da dama da suka hada da yaki da rashawa da alakarsa da tsaffin shugabannin kasa da kuma irin kudaden da ya kwato a tsohuwar gwamnatin kasar.