Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Shekara 10 da kirkirar shafin Twitter

A ranar Litinin din nan ce kafar sada zumunta ta Twitter ta cika shekara 10 da kafuwa.

A ranar 21 ga Maris na 2006 ne dai wasu matasa guda hudu wato Evan Williams da Noah Glass da Jack Dorsey da kuma Biz Stone suka kirkiri kafar, a San Francisco, da ke jihar California ta Amurka.

Sai dai an kaddamar da ita a watan Yulin shekarar.