Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Hare-haren bama-baman da aka kai Brussels

Kafar yada labarai ta Brussels ta ce an kai har-haren bama-bamai filin jirgin sama na kasar da kuma tashar jirgin kasa, al'amarin da ya yi sanadiyar rasa rayuka 13.

Bama-bamai biyu sun tashi ne a wajen da fasinjoji suke zama kafin tashin jirginsu da misalin karfe bakwai agogon GMT, wanda ya yi daidai da karfe takwas na safe a kasar.

Bayan sa'a guda kuma wani bam din ya tashi a tashar jirgin kasa ta Maalbeek metro station, da ke kusa da hukumar tarayyar Turai.

Tuni aka rufe wuraren da ala'marin ya faru.

Wadannan hare-hare na zuwa ne kwanaki hudu bayan da aka kama Salah Abdeslam a Brussels, mutumin da ake zargi da kitsa hare-haren Paris.

Gwamnatin Belgium ta tabbatar da cewa ba a bayar da ainihin adadin wadanda suka mutu ba a filin jirgin saman.

Har yanzu dai ba a san musabbabin harin ba. Amma an rufe baki daya tashar jirgin kasan da filin jirgin saman.

A yanzu dai Belgium ta ce barazanar ta'addancin kasar na matukar karuwa.