Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Gane Mani Hanya 26/03/2016

<span >A Najeriya, a baya-bayan nan ana samun rahotannin hare-haren kunar bakin wake inda 'yan kungiyar Boko haram ke amfani da mata da 'yan mata musamman a yankin arewa maso gabashin kasar.

Shin ko su wanene wadannan 'yan matan? Daga ina suke? Ta yaya ake shawo kansu har su amince su kai harin kunar bakin wake?

Bilkisu Babangida ta samu wata dama da ba kasafai ake samun irinta ba, inda ta tatttauna da daya daga cikin 'yan matan da Boko Haram ta so amfani da su wajen kai harin Bam a sansanin 'yan gudun hijira da ke garin Dikwa na jihar Borno da aka kai a baya-bayan nan.

An sauya sunan yarinyar tare da jirkita muryar ta, saboda wasu dalilai:

Ga rahoto na musamman da Bilkisun ta hada mana: