Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Wanda ya karkatar da jirgin Masar ya mika wuya

An kawo karshen karkatar da jirgin sama na kasar Masar da wani mutum ya yi, inda ya tursasa shi sauya akalarsa zuwa filin jirgin sama na Larnaca da ke Cyprus.

An saki dukkan fasinjojin da aka yi garkuwa da su an kuma kama mutumin da ya karkatar da jirgin.

Mutumin da ya karkatar da jirgin saman Masar MS181, ya yi ikirarin cewa yana sanye da jigidar bam ne.