Kamfanin wasan kwamfuta mallakar Facebook zai biya kwastomi kudi

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Na'urar wasan kwamfuta ta Oculus mallakar Facebook

Kamfanin wasan computer mallakar Facebook mai suna Oculus, yayi tayin mayar wa da wadanda suka yi odar wasanin nasa kudin da suka biya na aiko musu da wasannin a sakamakon jinkiri da aka samu.

An shirya aikawa da kashin farko na ababen wasannin ga wadanda suka yi odar a ranar 28 ga watan Maris, wanda ya wuce.

Kamfanin ya dora laifin jinkirin ga yankewar bazata na wani bangare na na'urar, sannan ya kara da cewa kwastomominsa za su samu labarin halin da ake ciki kan odar tasu a ranar 12 ga watan Afrilu.

A sakon da ya aika ta dandalin sada zumunta da muhawara na Twitter a kan mayar wa da kwastomomin kudinsu, shugaban kamfanin Oculus ya ce babban abin da zan iya yi a yanzu shi ne in samar masu da bayanan da suka kamata cikin gaggawa.

Na'urar wasan kwamfutar da ake sawa a ido mai kama da tabarau na dauke da wasanni masu kayatarwa.