Sanin Kai 2016: Ɗakunan gyaran gashin amare a Tokyo

Sanin Kai 2016: Ɗakunan gyaran gashin amare a Tokyo

Shin mene ne tasirin irin shigarka ko adon da kake yi? A ci gaba da shirin Sanin Kai na BBC, za mu leka ɗakunan gyaran gashi da ke birane a faɗin duniya. Mun je Tokyo domin gano sirrin da ke tattare da ɗakin gyaran gashi na amare.

Hitomi Tezuka, wadda ke zaune a hawa na biyar na jerin benayen kasuwar lardin Gotanda da ke birnin Tokyo, tana shirin ta sanya doguwar riga ta musamman wadda amare suke sanyawa. Ranar hutu ce a ƙasar , saboda haka birnin ya yi tsit. Ita da Takeshi Sasaki, saurayin da za ta aura ne kawai a shagon. Dukkan su ma'aikata ne, saboda haka sun yi amfani da ranar hutun ne wajen ɗaukar hotunan bikinsu.

Halayya wata aba ce mai mahimmanci a tsakanin wannan al'umma. Takeshi, angon nan gaba yana tsakiyar kayan turawa masu launin fink(pink) da fari, da ke rataye a shagon wadanda kuma aka yi wa adon tufafin kimono. Sutura ce da aka yi wa ado na faɗa wadda kuma kuɗinta zai iya kaiwa $9,000 wato kwatankwacin Fam dubu shida.

Tsadar suturar ce ta sanya mutane da dama suke san su karɓi hayar kayan, in ji Miyoko Nagaiwa, manajan ɗakin gyran gashin amare na Calane. Sau ɗaya tak ake sanya kayan, duk da cewa hayarsu akwai matuƙar tsada.

Hitomi, mace ce mai tafiya da zamani, ta fanni da dama. Aikinta shi ne horas da masu wasan ƙwallon Golf. Ta haɗu da mijin da ta aura ta kafar sada zumunta. Amma ita ma ta bari zamani ya ɗan guje mata.

" Na so na sanya tufafin kimono saboda al'adarmu ce," in ji Hitomi. Sau biyu kacal ta taɓa sanya irin suturar, kafin aurenta.

Ko da lokacin bikinta ma, ta yi niyyar sanya kayan turawa ne. Ana kwashe lokaci mai tsawo wajen sanya suturar, kuma ni ba na son mutane su daɗe suna jira na.

A duk lokacin da Hitomi ta sanya kayan da ta saba sa wa, tana fitowa ne daga bayan labule sannan ta zauna. Mata huɗu ne suka taru suke gyaran gashinta da yi mata kwalliya.

" Sabon gyaran gashi yanzu yana ɗaukar salo biyu wato na 'yan Japan da kuma na turawan yamma." in ji Maki Ishiguro, wata mai gyaran gashi, a lokacin da take kulla furen kainuwa a gashin Hitomi.

Dangantakar soyayya da gashi a al'adar mutanen Japan.

" A da can, yaran mata a Japan suna yanke gashinsu a duk lokacin da suka rasa masoyansu," in ji Hitomi. " Yanke gashinki yana nufin yanke duk wani abin da zai sa ki tuna baya, sabon al'amari ne."

Tana tara gashi saboda bikinta da za a yi a Yuli.

Ana sanya ido sosai kan yadda mata ke gyaran gashinsu, kuma har yanzu ana ƙyamar rina gashi, a wasu wuraren. Takeshi ya rina gashinsa a lokacin yana ɗalibi, amma yanzu ba zai yi hakan ba musamman tunda yana mu'amala da abokan cinikayya.

A matsayinta na mai wasan guje-guje a makarantar gaba da sakandare, Ana sa ran Hitomi za ta bar gashinta. " A gasar kwallon golf, mutum ba zai rina gashinsa ba saboda abin da ake tsammani shi ne ka mayar da hankalinka a kan wasan ba wai burge mutane ba," in ji ta " Gwara ka yi amfani da lokacin da kake da shi na rina gashi wajen inganta harkar wasan da kake yi."

Hakkin mallakar hoto Kayoko Nakashima

Ma'auratan sun fara fita bayan da Hitomi ta koyawa Takeshi wasu darussa kan wasan kwallon golf.

Takeshi ya ce yana ƙaunar "komai dangane da ita. "musamman ganin cewa dabi'arta mai kyau ce. Halayyarta irin ta al'adar Japan ce, saboda haka abin yana burge ni."

"halayya wata aba ce mai mahimmanci wajen rayuwa a Japan."

"Yana da kamun kai kuma yana ɗauka ta da wadda ta fi komi mahimmanci," in ji Hitomi da take magana a kan Takeshi.

Ta kuma nuna farin cikinta da yadda yake tafiyar da aikinsa. " Ban san abubuwa da yawa dangane da aikinsa ba amma dai ina ganin yana aiki kan jiki kan ƙarfi , wannan ne ma ɗaya daga cikin dalilan da yasa na ji ina ƙaunar sa." in ji Hitomi.

Hitomi ta zabi suturar kimono mai launin fari wadda kuma take da yanayin zalɓe, wani tsuntsu da yake nuna tsawon rai. Ta hada suturar da jambaki da sauran kayan kwalliyar amarya jajaye.

Takeshi ya ce launin fari da ja yana nuna shigar Hitomi ya zuwa sabbin iyalai.

"Farin launin yana nufin ta zama kamar yau aka haife ta, a inda shi kuma launin ja yake nuni da cewa ta zama sabuwar jini, wato ta bar iyalanta zuwa wani sabon iyalin." in ji shi.

Da zarar an ɗaura soson ɗamara, to fa an shirya sanya suturar kimono.

" Wannan ya yi kyau," ta ce, yayin da take duban kanta a madubi.

Ranar ta kasance mai zafi sosai, saboda haka ango da amaryar sun fita waje zuwa wurin bauta domin ɗaukar hoto a wajen.

Takeshi ya amince cewa wurin ibadar ba shi da wani mahimmanci sosai, a wurinsa. " Yin aure abu ne mai matuƙar mahimmanci," ya ce. " Wannan biki ne kawai."