Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Gane Mini Hanya 16/04/2016

Hakkin mallakar hoto Screen Grab

A ranar Asabar ne aka yi bikin cika shekaru 40 da kafuwar jami'ar Maiduguri da ke jihar Borno a yankin arewa maso gabashin Najeriya.

Kazalika an kuma gudanar da bikin yaye dalibai duk a ranar, wanda aka shafe shekaru da dama ba a yi ba saboda rikicin Boko Haram.

Shugaban jami'ar ta Maiduguri, Farfesa Ibrahim Abubakar Njodi ya kawo mana ziyara sashen Hausa na BBC, kuma Abdou Halilou ya yi hira da shi, inda ya fara da tambayarshi ko yaya rikicin kungiyar Boko Haram ya shafi aikace- aikacen jami'ar?