Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Gane mini hanya 23/04/2016

Yayin da dakarun tsaron kasashen yankin tafkin Chadi da suka hada da Nijeriya da Nijar da Kamaru da Chadi ke ci gaba da yaki da kungiyar Boko Haram, rundunar sojan sama ta Nijeriya ta ce bisa dukkan alamu, an kusa kammala yakin saboda irin nasara da ta ce ana samu kan masu tayar da kayar bayan, hatta a makarfafarsu dake dajin Sambisa.

To amma yayin da hukumonin tsaron ke ikirarin kusan mayar da Boko Haram ta zamo tarihi, tambayar da mutane da dama ke yi ita ce shin ina manyan shuwagabannin kungiyar ta Boko Haram da suka hada da jagoranta Abubakar Shekau, suke?

Wakilinmu Is'haq Khalid ya tattauna da babban hafsan sojin sama na Nijeriya, Air Marshall Sadique Abubakar, kan wannan batu.

To amma wakilin namu ya fara da tambayar shugaban sojin saman ne, ko shin yaya zai bayyana halin da rundunar sojan saman ta ke ciki, yayin da a wannan wata na Afirilu ta cika shekaru hamsin da biyu da kafuwa?