Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Cututtukan zuciya na barazana ga 'yan Afrika

Cututtukan zuciya na neman zama wata matsala da ke addabar mutane da dama a kasashen Afrika.

Amma yanzu an samu wani matashi a kasar Kamaru da ya kirkiro wata na'ura da zata nadi bayanai akan yadda zuciyar mutum ke aiki domin gano wata matsala tun da wuri.

Kuma hakan ya rage yawan mace-macen da ake samu daga ciwon zuciya.