Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

'Cin hanci ya mamaye Nigeria'

Kwamitin da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nada domin ya ba shi shawara kan yadda za a dakile matsalar cin hanci ya ce ya gano cewa matsalar ta mamaye kusan daukacin fannonin kasar.

Daya daga cikin 'yan kwamitin, Farfesa Sadik Isa Radda, ya shaida wa BBC cewa babban aikin kwamitinsu shi ne ya kalli halin da kasar ta fada sakamakon cin hanci da rashawa, sannan a samar da mafita.