Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Yanda 'yan hizba ke muzgunawa mutane a Saudiya

A kwanakin baya ne hukumomi a Saudiyya suka rage karfin ikon da 'yan Hisbah ke da shi. Wata sabuwar doka da aka yi ta hana 'yan Hisba bin mutanen da ake zargi da aikata laifuka a guje ko kama su. Ana zargin 'yan Hisbah da wuce-gona-dairi. Sai dai ba kowane dan kasar ne ke murna da sabuwar dokar ba. Daga Riyadh, ga rahoton Hanan Razek.