Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Nigeria ta shahara a cin hanci — Cameron

An dauki hoton bidiyon Pira ministan Birtaniya, yana wata katobara, inda yake shaidawa Sarauniyar Ingila, cewar shugabanin wasu kasashen da suka fi bala'in cin hanci za su halarci taron kolin da zai bakunta a ranar alhamis a kan yaki da cin hanci.

David Cameron, ya bayyana Najeriya da Afghanistan a matsayin kasashe biyu da matsalar cin hanci da rashawa ta fi kamari a duniya.

Ba a dai sani ba ko Mista Cameron din yana da masaniyar cewa ana nadar kalaman nasa ko kuma a'a.