'Yan gudun hijirar Syria a Ghana
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

'Yan gudun hijirar Syria a Ghana

Yakin da ake yi a Syria na tilasta wa mutanen kasar da dama yin gudun-hijira zuwa sassan duniya, musamman kasashen Turai don tsira da ran su.

Yayin da wasu kasashen Turai ke rufe kofa ga 'yan gudun hijirar Syria, hankalin wasu daga cikinsu ya fara karkata yammacin Afirka sakamakon karbar da suke samu.

Wakilin BBC Thomas Naadi ya zanta da wasu iyalai da suka samu matsuguni a birnin Accra na kasar Ghana.