Shekara 25 da samun 'yancin kan Somaliland
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Shekara 25 da samun 'yanci Somaliland

Bayan mummunan yakin basasa shekara 25 a Somaliya, arewa maso yammacin kasar ya bangare daga sauran sassanta , a inda ta zama kasa mai cin gashin kanta.

Kuma har yanzu, babu wata kasa guda daya da ta amince da kasar ta Somaliland.

To amma yankin mai al'umma kimanin miliyan 3.5, na daya daga cikin yankunan da suke da tsayayyiyar dimokradiyya a kusurwar nahiyar Afirka.